Qatar ta fitar da wasu sabbin dokokin bayar da biza ga ƴan Najeriya da nufin magance matsalar zaman da ya wuce ƙa’ida a cikin ƙasar ta yankin Gulf, ciki har da sharaɗin daina baiwa maza ƴan Najeriyar izinin shiga ƙasar face suna tare da iyalansu.
Wata sanarwa da gwamnatin Qatar ta fitar game da sabbin dokokin bayar da izinin shiga ƙasar ne ke bayyana wannan mataki kan ƴan Najeriya a wani yunƙuri da ƙasar ke yi don tsaftace harkokin shige da fice dai dai lokacin da ta buɗe ƙofa ga masu zuba jari da kuma ɗaukar ma’aikata daga ƙetare.
Gwamnatin ta Qatar ta kafa hujja da yadda ƴan Najeriyar kan yi zaman dirshan da zarar sun samu izinin shiga ƙasar ba tare da fita ba koda wa’adin zamansu ya kawo ƙarshe.
Ƙarƙashin waɗannan sabbin dokoki dole sai ƴan Najeriyar sun nuna tanadinsu na tikitin dawowa da kuma Otel ɗin da zasu sauka gabanin samun bizar.
Ma’aikatar cikin gida a Qatar ta ce wajibi ne matafiyan su tanadi ɗakunan kwana a Otel mai daraja ta biyu da aka fi sani da five star hotels.
A cewar ma’aikatar, wannan sabon tsrai ya shafi hatta mutanen da ke kan layi a nemi bizar shiga ƙasar ta yankin gabas ta tsakiya.
Dubban ƴan Najeriya ne ke halartar Qatar kowacce shekara walau a batutuwa masu alaƙa da kasuwanci ko kuma karatu ko ma aikatau.
