Rundunar ’Yan Sandan Jihar Kaduna ta gayyaci tsohon gwamnan jihar, Malam Nasir El-Rufai, tare da wasu manyan membobin jam’iyyar African Democratic Congress (ADC), bisa zargin haifar da tashin hankali a cikin al’umma.
A cewar wata takarda da aka gani, wadda ya sanya wa hannu Mataimakin Kwamishinan ’Yan Sanda mai kula da Sashen Binciken Laifuka (CID), Uzainu Abdullahi, an umurci shugaban ADC na jihar Kaduna da ya gabatar da El-Rufai da wasu mutane a Sashen Binciken Laifuka na Jihar (SCID) a ranar 8 ga Satumba, shekarar da muke ciki.
Waɗanda aka gayyata sun haɗa da Bashir Sa’idu, Jafaru Sani, Ubaidullah Mohammed (wanda aka fi sani da “30”), Nasiru Maikano, Aminu Abita, da Ahmed Rufa’i Hussaini (wanda aka fi sani da “Mikiya”). Takardar ta ɗauke da alamar tuhumar “Binciken Laifuka: Shari’ar Haɗa Kai, Tayar da Zaune Tsaye, da Haifar da Mummunar Rauni,” ta bayyana cewa an gayyaci mutanen don bayyana zarge-zargen da wasu masu ƙorafi suka gabatar.
Sai dai kuma, membobin ADC sun ce ba a ba su takardar gayyatar ba, kuma sun ji labarin ta hanyar kafofin watsa labarun kawai. Wannan matakin ya haifar da cece-kuce a siyasance a jihar, inda wasu ke kallon sa a matsayin wani shiri ne ga masu sukar gwamnatin jihar Kaduna.
