Rwanda ta buƙaci Majalisar ɗinkin duniya ta yi watsi da koken maƙwabciyarta Jamhuriyyar Demokradiyyar Congo da ke neman ayyana Kigali a matsayin wadda ta jagoranci kisan ƙare dangi a ƙasar ta hanyar ɗaukar nauyin mayaƙan M23 waɗanda har yanzu ke ci gaba da kashe-kashe a wannan ƙasa ta Afrika.
A farkon shekarar nan ne mayaƙan na M23 waɗanda ke samun goyon bayan Rwanda suka kutsa gabashin Congo tare da ƙwace manyan garuruwa masu tasiri ga tattalin arziƙi da tsaron ƙasar.
Wannan hare-hare na mayaƙan M23 ya kai ga kisan ɗimbin mutane kama daga fararen hula da kuma dakarun ƙasar har ma dana ƙawancen ƙasashen kudancin Afrika, dalilin da ya sanya mahukuntan Kinshasa neman Majalisar ɗinkin duniya ta yi wannan hukunci na ayyana Rwanda a matsayin wadda ta ɗauki nauyin kisan ƙare dangi a ƙasar.
Sai dai Rwanda ta ce wannan zargi ne maras tushe, bayan da take ci gaba da musanta hannunta a taimakon mayaƙan na M23.
