Gwamnatin tarayya ta ce kammala aikin sabbin gine-gine a Asibitin koyarwa na Aminu Kano, zai kara saukaka yadda al’umma ke turuwa zuwa kasashen ketare domin neman Lafiya.
Mataimakin shugaban majalisar dattawan kasar nan Sanata Barau Jibrin ne bayyana hakan, a ziyarar duba wasu gine-gine da gwamnatin tarayya ke yi karkashin jagorancin shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu.
Sanata Barau Jibrin ya ce kammala ayyukan zai kara saukakawa, da kuma kawo karshen zuwa kasashen ketare domin neman lafiya.
A nasa jawabin shugaban asibitin koyarwa na Aminu Kano, Farfesa Abdurahama Abba Shehe, ya ce dama asibitin na bukatar irin sabbin ayyukan wanda zai kara inganta ayyukan da ake gudanarwa.
Cikin ayyukan da gwamnatin tarayya ke shirin kammalawa sun hadar da sashen kula da bangaren yara da kammala dakunan kwanan dalibai da kuma karin wasu gine-gine da zasu sake daga likkafar asibitin koyarwa na Aminu Kano.
