Wasu alƙaluma sun nuna yadda gwamnatin jihar Sokoto ta kashe kuɗin da ya kai naira biliyan 9 da miliyan 900 wajen sayen motoci na alfarma adadin da ke matsayin kusan rabin kuɗaɗen shigar da jihar ta samu a shekarar 2024.
Wannan na zuwa a dai dai lokacin da jihar ta yankin arewa maso yammacin Najeriyar ke fama da tarin matsaloli kama daga baƙin talaucin da ya addabi jama’arta da kuma ƙarancin ruwan sha da ake fama da shi dama lalacewar asibitoci koma ilahirin ɓangarorin kula da lafiya duk kuwa da ƙalubalen lafiyar da ake fuskanta.
Kamar yadda ya ke ƙunshe cikin kasafin da Jariodar SolaceBase da ake wallafawa a jihar Kano ta Najeriyar ta ruwaito, gwamnatin ta Sokoto ta sahale sayo motocin alfarma samfurin Prado ƙirar 2023 har guda 30 da kuɗinsu ya kai naira biliyan 7 da miliyan 464 don rarrabawa mambobin majalisar zartaswar jihar.
Sai kuma wasu ƙarin motocin ƙirar Changan har guda 40 da aka siya kan kuɗi naira biliyan 2 da miliyan 514 don rabawa mashawartan gwamna na musamman.
A jumalace kuɗin sayen waɗannan motoci aƙalla 70 ya kai naira biliyan 9 da miliyan 978.
Jihar Sokoto ta tattara kuɗaɗen shiga na cikin gida da suka kai naira biliyan 22 da miliyan 46 a shekarar 2024, kuɗin da aka yi tunanin gwamnatin ta yi amfani da su wajen magance ɗimbin matsalolin da suka dabaibaye jihar, musamman ɓangaren ilimi lafiya da kuma rashin wadataccen ruwa ga jama’a.
Wasu alƙaluma da hukumar ƙididdiga ta Najeriyar NBS ta fitar ya nuna cewa Sokoto jiha mafi fama da talauci a ƙasar inda ake da mutane miliyan 5 da dubu 800 da ke cikin matsanancin talauci mafi yawan adadi da wata jiha ke da shi.
