Tinubu ya kawar da matsalar rashin biyan albashi a jihohi 27 — Mohammed Idri
Ministan Yaɗa Labarai, Mohammed Idris, ya bayyana cewa sauye-sauyen da Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya aiwatar sun kawo ƙarshen matsalar biyan albashi a jihohi 27.
Ya yi wannan bayani ne a Abuja yayin da kwamishinonin yaɗa labarai daga jihohi 36 suka kai masa ziyara.
Idris ya ce manufofin shugaban suna tafiya ne don amfanin ƙasa baki ɗaya, ba siyasa ba, tare da tabbatar da cewa ayyuka suna gudana a dukkan jihohi ba tare da nuna bambanci ba.
Ministan ya ce cire tallafin man fetur ya buɗe sabbin hanyoyin samun kuɗaɗe ga jihohi, wanda ya taimaka musu wajen aiwatar da muhimman ayyuka.
Ya ƙara da cewa kafin Tinubu hauhawa mulki, kaso 97 cikin 100 na kuɗaɗen shiga na tarayya ana amfani da su wajen biyan bashi, abin da ya hana jihohi biyan albashi yadda ya kamata.
Idris ya yi kira ga gwamnatocin jihohi da su yi aiki tare da shugaban kasa wajen tabbatar da cigaban ƙasa. Haka kuma ya sanar da cewa ma’aikatarsa za ta kai ziyara zuwa wasu jihohi domin duba ayyukan da ake yi da kuma jin ra’ayin jama’a.
Shugaban taron kwamishinonin yaɗa labarai, Usman Tar daga jihar Borno, ya ce sun yi alkawarin inganta haɗin kan ƙasa ba tare da la’akari da jam’iyya ko bambancin siyasa ba.
