Trump ya shigar da ƙarar jaridar New York Times tare da neman diyyar dala biliyan 15
Shugaba Donald Trump na Amurka, ya nemi diyyar dala biliyan 15 daga kafar yaɗa labarai ta New York Times da wasu ma’aikatanta guda 4 kodayake tuni kafar ta yi watsi da wannan ƙara bayan da ta ce bata cika sharuɗɗan da ya kamata ba.
Tun a Litinin ɗin farkon makon ne kotun yanki a birnin Florida ta aike da wannan tuhuma ga New York Times, dangane da wasu dogayen rubutu da kafar ta yi dama wani littafi guda da aka wallafa kuma jaridar ta buga a shafinta wanda ke caccakar Trump dama nasarar shi a zaɓen ƙasar na 2024.
Ƙarar ta bayyana wasu ƴan Jaridun New York Times a matsayin waɗanda suka ɗauki tsawon lokaci suna adawa tare da ɓata sunan shugaba Donald Trump.
Sai dai Jaridar bata bayar da amsa game da wannan ƙara ba, yayinda wasu majiyoyi suka jiyo shugabancinta na cewa babu ƙanshin gaskiya a dukkanin tuhume-tuhumen Trump kuma ba abi tsarin doka wajen shigar da ƙarar ko kuma miƙa mata tuhumar ba.
Baya ga New York Times Trump ya kuma nemi kafar Labarai ta Wall Street Journal ta biya shi diyyar dala biliyan 10 wadda itama ya ce ta ɓata masa suna bayan wallafa labarinsa kan lalata da kuma ƙarya akan dukiyarsa.
