Kotu a Ghana ta zartas da hukuncin ɗaurin shekaru 96 kan wasu ƴan Najeriya 3 da aka samu da laifin satar motoci a birnin Kumasi na lardin Ashanti.
Ƴan Najeriyar 3 da aka bayyana sunansu da Francis Friday da Linus Agwazie da kuma Russell Ekenze waɗanda aka kame tun a ranar 20 ga watan Yuni bayan da aka zarge su da satar motoci a wajen ajiyar ababen hawa.
Kakakin ƴansandan lardin Ashanti, Godwin Ahianyo, ya ce an miƙa mutanen gaban kotu tun a ranar 22 ga watan Yuli kuma bayan fara yi musu shari’a ne aka tabbatar da laifinsu.
Wannan hukunci na zuwa a dai dai lokacin da mahukuntan Ghana ke ci gaba da korar ƴan Najeriyar zuwa gida saboda tuhumarsu da aikata laifuka.
Ko a watan Mayun shekarar nan sai da wata kotu a Tarkwa ta aike da wata ƴar Najeriya gidan yari na shekaru 20 bayan samunta da laifin safarar wasu yara 4 don sanya su a harkar karuwanci.
Haka zalika ko a watan Yuli a watan Yulin shekarar nan, hukumar tsaron kan iyaka ta Ghana ta kame wasu ƴan Najeriyar 50 bayan samunsu da laifin damfara ta intanet da kuma safarar bil’adama.
