Mahukuntan Isra’ila sun tabbatar da kisan mutane 6 a wani hari da aka kai gabashin birnin Jerusalem yau Litinin, harin da ake alaƙantawa da matsin lambar sojoji da Yahudawan kama wuri zauna a yammacin gaɓar kogin Jordan.
Jami’an lafiya a Isra’ila sun ce mutane 12 ne suka jikkata a harin ciki har da wasu 6 da ke cikin mawuyacin hali, sai kuma wasu da dama da rauninsu bai yi girman da za a kaisu ga asibiti ba.
Tuni gwamnatin Isra’ila ta bayyana harin a matsayin na ta’addanci, kodayake babu wata ƙungiya da ta ɗauki alhakin kai shi.
Da sanyi safiyar yau ne wasu Mahara suka farwa wata motar safa a mahaɗar Ramot inda nan take suka buɗe wuta, kuma nan take ƴansanda suka kashesu bayan ta’adin da suka yiwa ƙasar.
Tuni masana suka fara sharhi kan wannan hari, wanda sabon abu ne a Isra’ila kafin faro yaƙinta a Gaza wanda zuwa yanzu ta kashe mutanen da yawansu ya haura dubu 60 ciki har da fiye da 40 a safiyar yau kaɗai.
Ƴansanda sun ce Maharan sun sauka a babura masu ƙafa biyu gabanin buɗe wutar.
Tuni Isra’ila ta yi umarnin kulle shingayen binciken ababen hawa da ke tsakanin gabanin Jerusalem da Yammacin gaɓar Kogin Jordan.
Ƴansandan Isra’ila sun ce Maharan sun fito ne daga Yammacin gaɓar Kogin Jordan kuma tuni gwamnatin ta sanar da wasu sumame kan ƙauyukan da ake sa ran maharan sun fito da suka ƙunshi Qatana da Biddu da kuma Beit Inan da kuma Beit Duqu.
Firaminista Benjamin Netanyahu a jawabinsa bayan ziyartar wajen da harin ya faru, ya ce dole su ɗauki mataki don hana sake faruwar harin a nan gaba, yayinda ministan tsaro Ben-Gvir ke cewa wajibi ne kowanne Bayahude ya mallaki makamai don kare kansa.
