Wani taron tsaro da aka shirya a Katsina ƙarƙashin Katsina Security Community Initiative ya rikide zuwa tarzoma bayan wasu ‘yan daba da ake zargin masu goyon bayan siyasa ne suka tarwatsa shi.
Taron, wanda ya haɗa kwararru daga bangarorin tsaro, tsoffin jami’an soji da ’yan sanda, masana da shugabannin al’umma, an shirya shi ne domin tattauna hanyoyin magance matsalar tsaro da ta addabi jihar.
Jaridar Daily Trust ta rawaito cewa rikicin ya fara ne lokacin da mai shirya taron, Dr. Bashir Kurfi, yake bayyana matsalolin tsaro a jihar, inda wani ya katse shi da zargin cewa yana sukar gwamnati. Sai sauran ‘yan daba suka tada rikici, suka jefa kujeru, suka kai hari ga ‘yan jarida, har ma wasu daga cikinsu suna rike da makamai.
Bayan taron ya tarwatse, masu shiryawa sun zargi gwamnati da hannu a lamarin, suna mai cewa wasu shugabannin ƙananan hukumomi da aka gani a wajen suna tattaunawa da ‘yan daban, har ma suna ba su kuɗi.
Sai dai Kwamishinan Yaɗa Labarai da Al’adu na jihar, Dr. Bala Salisu Zango, ya ce bai san da taron ba balle tarzomar, don haka ba zai yi tsokaci ba.
