Rundunar ‘yan sanda ta jihar Oyo ta sanar da ceto wani ɗan ƙasar Masar da aka sace a safiyar ranar 8 ga Satumba, yankin Alomaja da ke Idi-Ayunre, Ibadan.

A cewar kakakin rundunar, CSP Adewale Osifeso, Rundunar ƴansandan ta ceto wanda aka sace cikin sa’o’i 24 ba tare da an biya kuɗin fansa ba. Ayyukan ceto ya haɗa da jami’an 4 PMF Ibadan, ƙwararrun ƙungiyar leƙen asiri da dabaru, tare da ‘yan banga na gida da kuma haɗin gwiwa da rundunar ‘yan sandan jihar Ogun.

An ceto wanda aka sace ba tare da kuɗin fansa ba kuma an kai shi Asibitin ‘Yan Sanda, Eleyele, don kulawar likita, kafin a haɗa shi da iyalansa.

Rundunar ‘yan sandan ta Oyo ta kuma bukaci jama’a da su kasance a ankare da kuma su ba da rahoton duk wani abu mai shakku ga ‘yan sanda ta lambobin gaggawa, suna mai jaddada cewa kiyaye lafiyar jama’a shine babban abin da suke so, kuma sun himmatu wajen tabbatar da zaman lafiya a jihar Oyo ga kowa.

Share.
Leave A Reply

Exit mobile version