Ma’aikatar ilimi ta bayyana cewa daga yanzu ba dole ba ne sai ɗaliban da ba su da alaƙa da kimiyya da fasaha sun ci darasin lissafi a jarabawarsu ta kammala sakandire kafin samun gurbin karatu a manyan makarantun ƙasar.

Wannan na ƙunshe ne cikin wata sanarwa da daraktar yaɗa labaran ma’aikatar ilimin tarayyar Najeiyar, Folasade Boriowo, ta sanya wa hannu a Talata, inda take cewa gwamnatin ƙasar ce ta amince da sabon tsarin gyaran sharuɗan karɓar ɗalibai a dukkan manyan makarantun ƙasar, domin sauƙaƙa samun damar shiga jami’a da sauran cibiyoyin ilimi.

Sanarwar ta bayyana cewa wannan mataki ya shafi jami’o’i, kwalejojin kimiyya da fasaha da na koyon malanta da kuma cibiyoyin koyon sana’o’i a faɗin ƙasar.

Bugu da ƙari, sanarwar ta ruwaito ministan ilimi na ƙasar Tunji Alausa yana cewa wannan mataki ya zama tilas bayan shekaru da aka kwashe ana daƙile waɗnɗ suka da hazaƙa daga shiga jami’a.

A baya dai, ɗalibai da dama sun haƙura da karatu saboda gaza cin darasin lissafi a makarantun sakandire, sai dai wani tsagi na masharhanta na ganin matakin zai taimaka wa fannin ilimi a ƙasar.

 

Share.
Leave A Reply

Exit mobile version