Sakamakon wani bincike da hukumar NDHS ta gudanar ya nuna yadda Najeriya ta samu raguwar haife haife a shekarar da ta gabata ta 2024 zuwa kashi 4.3 cikin dari daga kashi 5.3% da kasar ke gani a baya.
Wannan sakamako ya nuna canjin a alkaluman da Najeriyar ke tattarawa na yawan haihuwa a sassan kasar mafi kololuwa cikin shekaru 5 da suka gabata.
Karamin ministan lafiya na Najeriyar Iziaq Salako da ke sanar da hakan yayin zaman taron kaddamar da wannan rahoto da ya gudana Abuja, ya ce Najeriya ta samu wannan raguwar haife haife ne sakamakon karuwar matan da suka rungumi tsarin tazarar iyali daga kashi 12% a 2018 zuwa 15% a 2023.
An kuma samu karuwa a yawan matan da suka samu gamsuwa a dalilin amfani da dabarun bada tazaran haihuwan zuwa kashi 37%.
Karamin Minustan lafiyar na Najeriya ya bayyana ci gaban a matsayin gagarumar nasara kodayake ya ce har yanzu akwai aikin da ya kamata a yi domin inganta rayuwar mutane da tattalin arzikin kasar baki daya.
Salako ya ce an samu karuwar kashi 63% a yawan matan dake zuwa asibiti yin awon ciki, mata kashi 46% ne ke haihuwa tare da taimakon kwararrun Ungo zoma, mata kashi 42% a 2024 ne ke samun kula bayan kwanaki biyu da haihuwa daga kashi 38% a 2018.
