Hukumomin Spain sun yi barazanar cewa da yiwuwa ƴan wasan tawagar ƙasar ba za su halarci gasar kofin duniya ta badi ba, idan har Isra’ila ta samu tikitin shiga gasar.
A cewar mai magana da yawun jam’iyyar Socialist Workers mai mulki a ƙasar ta Spain, Patxi Lopez, za su nazarci lamin yadda ya kamata.
Wannan dai na daga cikin matakan da Spain ɗin ke ɗauka na nuna rashin goyon bayanta ga hare-haren da Isra’ila ke kaiwa yankin Gaza, wanda a farkon wannan makon Majalisar Ɗinkin Duniya ta tabbatar da cewa Isra’ilan na aikata kisan ƙare dangi ne ga Falasɗinawa.
Rabon da Isra’ila ta halarci gasar lashe kofin duniya tun a shekarar 1970.
To sai dai akwai yuwuwar a gasar da za a yi a baɗi a ƙasashen Mexico da Canada da kuma Amurka ta samu tikitin halarta, ganin cewa a yanzu tana mataki na uku a rukunin neman gurbi shiga gasar na hukumar kwallon ƙafar Turai, maki ɗaya da Italiya duk da cewa ta fi tawagar Italiyan yawan wasanni.
RFI HAUSA
