Gwamna Abba Kabir Yusuf buƙaci majalisar dokokin jihar ta haramta abubuwan da suka shafi auren jinsi a jihar.

Abba Kabir Yusuf ya buƙaci matakin hakanne bayan taron majalisar zartarwar jihar da aka gudanar ranar Laraba.

Cikin ƙudurorin da majalisar zartarwar ta aike wa majalisar dokokin – wanda kwamishina Abduljabbar Mohammed Umar ya sanya wa hannu, ta buƙaci da majalisar ta amince da bukatar gwamnatin jihar na ɗaukar mataki tare haramta duk wani abu da ya shafi auren jinsi a a faɗin jihar.

Jihar Kano da ke arewacin Najeriya na daga cikin jihohin ƙasar da ke amfani da shari’ar addinin musulunci – wadda a dokokinta suka haramta auren jinsi, tare da tanadar hukunci mai tsanani ga wanda ya aikata.

Share.
Leave A Reply

Exit mobile version