Kwamandojin ƙungiyar ta’addanci ta Ansaru sun gurfana gaban kotu a Abuja

Hukumar tsaron farin kaya ta DSS a Najeriya ta sanar da gurfanar da wasu manyan kwamandojin ƙungiyar ta’addanci ta Ansaru a gaban babbar kotun Tarayya da ke Abuja fadar gwamnati, waɗanda za su fuskanci mabanbantan tuhume-tuhume masu alaka da ta’addanci.

Manyan kwamandojin biyu na Ansaru an bayyana sunayensu da Mahmud Usman wanda aka fi sani da Abu Bara’a Abbas ko kuma Mukhtar tare da mataimakinsa Mahmud Al-Nigeri da aka fi sani da Malam Mamuda.

DSS ta gabatar da shafuka 32 na hujjojin da ta ke da su kan aikata ayyukan ta’addanci kan kwamandojin na Ansaru guda biyu gaban mai shari’a Emeka Nwite da ke jagorantar zaman na yau a babbar kotun Najeriyar.

Cikin tuhume-tuhumen da waɗannan kwamadoji na Ansaru ke fuskanta har da kitsa ɓalle gidan yarin Kuje a cikin watan Yulin 2022 wanda ya kai ga tserewar fursunoni fiye da 600.

Haka zalika mutanen biyu suke da hannu a hari kan dakarun Sojin Najeriya da ke sansanin wucin gadi na Wawa Cantonment a Kainji na jihar Neja cikin shekarar 2022.

Bugu da ƙari DSS ta yi zargin cewa kwamandojin biyu sun kuma samu cikakken horo kan ayyukan ta’addanci da sarrafa makamai da ma tashin bama-bamai a sansanonin ƴan ta’adda da ke ƙasashen Mali da Libya, yayinda suke taka muhimmiyar rawa wajen safarar makamai da rarrabasu har ma da horar da mutane dabarun ta’addanci.

DSS ta ce Mamuda ya samu nashi horon a sansanonin ƴan ta’addan tsakanin shekarar 2013 zuwa 2015.

Bugu da ƙari DSS ta ce waɗannan ƴan ta’adda guda biyu na da hannu wajen mabanbantan sace-sace da garkuwa da mutane da ke faruwa a sassan Najeriyar, ciki har da fitaccen Injiniyan Faransa a shekarar 2013 Francis Collomp da kuma Alhaji Musa Umar Uba, Magajin Garin Daura a shekarar 2019.

Sai kuma sauran manyan laifuka masu alaƙa da fashi da makami da yunƙurin hari kan cibiyar Uranium a Nijar.

Share.
Leave A Reply

Exit mobile version