Hukumar Kula da Wutar Lantarki ta Najeriya (NERC) ta fara amfani da wani sabon tsari da zai bai wa masu amfani da na’urorin samar da wutar lantarki ta hasken rana (solar) damar sayar da ƙarin wutar da suke samarwa ga kamfanonin rarraba wutar lantarki.
NERC ta bayyana hakan ne a wani saƙo da ta wallafa a shafinta na X, inda ta ce idan na’urar solar ta kwastoma na samar da wutar lantarki fiye da buƙatarsa, zai iya sayar da ƙarin wutar ga kamfanin rarraba lantarki (DisCo) tare da samun kuɗin da ya dace.
A cewar hukumar, ana kiran wannan tsari da “Prosumer”, wato tsarin da ke bai wa mutum damar kasancewa mai amfani da wutar lantarki tare da zama mai samar da ita a lokaci guda.
Sai dai NERC ta ce akwai wasu sharuɗɗa da dole a cika kafin shiga tsarin. Daga ciki akwai kasancewa kwastoma a wani kamfanin rarraba lantarki da kuma mallakar na’urar solar mai ƙarfin aƙalla 50kWp.
Haka kuma, mai son shiga tsarin dole ne ya samu amincewa daga kamfanin rarraba lantarki da yake ƙarƙashinsa, ya rattaba hannu kan yarjejeniyar tsarin, sannan ya yi rajista da NERC.
Sai dai hukumar ta bayyana cewa wannan tsari ba ya shafar gidaje da ƙananan masu amfani da solar da ake amfani da su a gidaje na yau da kullum.
Majiya: BBC HAUSA
