Hukumar Kula da Inshorar Lafiya ta Kasa ta kaddamar da shirin bayar da kulawar lafiyar gaggawa kyauta ga yara a Asibitin Koyarwa na Aminu Kano dake nan Kano.
Shirin, a cewar Darakta a hukumar, Dr. Salahudeen Sikiru, wani bangare ne na fadada shirin lafiyar iyaye da hukumar ke aiwatarwa zuwa ga yara masu rauni da masu bukata ta musamman.
Ya ce an fara shirin fiye da shekara ɗaya da ta gabata da nufin rage mace-macen jarirai ’yan kasa da shekaru biyar.
Ya kuma ce a karkashin shirin, yara da ke fama da matsalolin gaggawa kamar rashin numfashi, amosanin jini, cutar shawara da yaran da aka haifa bakwaini da ma cututtukan da ke buƙatar tiyata za su samu kulawa kyauta.
Daraktan ya kara da cewa duk yaran da ya sami kulawar gaggawar kuma, za a saka shi cikin shirin inshorar lafiya na NHIS, inda hukumar za ta ci gaba da biyan kudin inshorar don tabbatar da samun kulawar lafiya mai inganci.
