Masana a fannin diflomasiyya na ci gaba da tsokaci game da matakin ƙasashen haɗakar AES da suka ƙunshi Nijar Mali da kuma Burkina Faso na sanar da shirin ficewa daga kotun hukunta manyan laifuka ta duniya ICC.

Kotun ta ICC mai shalkwata a birnin Hague na Netherlands a shekarar 2002 ne aka samar da ita, da nufin saurara tare da aiwatar da hukunci kan manyan laifuka walau tsakanin shugabanni ko jagororin ƙasashe ko kuma abin da ya shafi rikici tsakanin ƙasashe biyu da ya kai ga yaƙi ko babban rikici.

Sai dai wata sanarwa da ƙasashen 3 suka fitar game da shirin ficewarsu daga wannan kotu mai mambobi fiye da 140 sun bayyana kotun ta ICC a matsayin wani makami da ake amfani da shi wajen aiwatar da mulkin mallaka ta fuskar tsaro da tattalin arziƙi har ma da siyasar ƙasashe.

A cewar sanarwar tuni ƙasashen 3, suka miƙa buƙatar ficewarsu daga kotun a hukumance, kodayake bisa ƙa’ida sai bayan shekara guda da miƙa irin wannan buƙata ne ƙasa ke iya ficewa daga kotun a hukumance.

Ƙasashen na Nijar Mali da Burkina Faso waɗanda dukkaninsu sojoji ke jagorantarsu bayan juyin mulki, na ci gaba da nesanta kansu da ƙasashen yammaci ta yadda suke ƙarfafa alaƙa da wasu ƙasashe irin Rasha.

Sojojin waɗanda suka ƙwace mulki daga fararen hula a Bamako da Ouagadougou da kuma Niamey a tsakanin shekarun 2020 zuwa 2023 na ci gaba da ƙarfafa alaƙar da ke tsakaninsu bayan yanke hulɗa da uwar goyonsu Faransa, a wani yanayi da dukkaninsu matsalolin tsaro suka yi musu katutu.

A cewar sanarwar ya tabbata cewa kotun ba zata iya tabbatar da adalci kan tarin laifuka masu alaƙa da laifukan yaƙi ko na cin zarafin bil’adama ko kuma kisan ƙare dangi da sauran manyan laifukan da ake ci gaba da aikatawa ba tare da kotun ta iya taka musu birki ba.

Share.
Leave A Reply

Exit mobile version