Ɗan majalisar wakilai, Abdulmumin Jibrin, ya bayyana cewa tsohon gwamnan Jihar Kano, Rabiu Musa Kwankwaso, bai rufe kofar shiga jam’iyyar APC ba gabanin zaɓen 2027.

Jibrin, jigo a jam’iyyar NNPP, ya ce Kwankwaso har yanzu ya bar kofar tattaunawa a bude da Shugaba Bola Tinubu da jam’iyyar APC, duk da kasancewarsa ɗan takarar shugaban kasa a zaɓen 2023.

Ya bayyana hakan ne a shirin Politics Today na gidan talabijin na Channels inda ya ƙara da cewa ƙungiyar Kwankwasiyya ƙarfin siyasa ce da ba za a iya watsi da ita ba.

Sai dai ya nuna yiwuwar wasu masu ruwa da tsaki a APC na Kano na iya hana shigar Kwankwaso saboda muradunsu na siyasa.

Jibrin, wanda ya sha ganawa da Shugaba Tinubu, ya ce komai yana yiwuwa a siyasa, duk da kasancewarsa ɗan Kwankwasiyya.

A zaɓen 2023, Kwankwaso ya samu kuri’u sama da miliyan ɗaya da ɗari huɗu, inda ya zo na huɗu, yayin da Tinubu ya lashe zaɓen da kusan kuri’u miliyan tara.

Share.
Leave A Reply

Exit mobile version