Abdulmuminu Jibrin kofa Dan majalisar wakilai mai wakiltar Kiru/Bebeji a majalisar wakilai ya sanar da ficewa daga jam’iyyar NNPP mai mulki a jihar Kano, inda ya amince da matakin korar sa da shugaban jam’iyyar ya sanar.

Dan Majalisar ya bayyana haka ne a wata sanarwa da ya fitar, inda a ciki ya bayyana cewa bai cancanci kora daga jam’iyyar ba, ba tare an ba shi damar kare kansa ba.

Tun da farko, jam’iyyar ce ta sanar da cewa ta kore shi bisa zarginsa da karya dokokinta.

Inda ya faɗi cewa, “na yi mamakin ganin an kore ni daga NNPP. Na yi amannar cewa tattaunar da na yi ba su yi nauyin da za su ja min kora ba,” in ji Kofa, inda ya ƙara da cewa “ba zan janye komai ba a cikin abin da na fada.”

Ya ce ba a gayyace shi ba domin ya kare kansa kan abin da ake zarginsa da aikatawa, “ko a mulkin soja, ana ba wanda ake zargi dama ya kare kansa.”

Ya ce ya so a ce ya ci gaba da zama a jam’iyyar, “Amma tunda jam’iyyar ta kore ni, dole in amince da matakin da ta dauka.”

Dan majalisar ya ce nan gaba kadan zai sanar da matakin da zai dauka a game da makomarsa a siyasa.

Share.
Leave A Reply

Exit mobile version