Alƙaluman waɗanda ke kamuwa da cutar Ebola a Congo ya ƙaru da fiye da ruɓaye guda cikin mako guda da sake samun ɓullar annobar cutar Lardin Kasai na kudancin jamhuriyyar Congo.

Hukumar lafiya ta Afrika ta ce akwai fargaba matuƙa kan saurin yaɗuwar wannan cuta duk da matakan da mahukuntan ƙasar ke ɗauka.

Cibiyar yaƙi da cutuka masu yaɗuwa ta CDC ta ce daga adadin masu ɗauke da cutar 28 da ake dasu a farkon mako, adadin ya kai 68 a yanzu ciki har da wasu mutane 16 da cutar ta kashe.

 

A cewar CDC yanzu haka akwai ɗimbin mutane da ake sanya idanu akansu saboda fargabar yiwuwar sun harbu da cutar, inda aka killace su don kange yiwuwar yaɗata ga wasu mutane.

Hukumomin lafiyar Congo sun ce cutar ta yaɗu daga yankuna 2 zuwa 4 a yankin na kudanci, duk da yadda mahukunta suka sanya dokar taƙaita zirrga-zirga a yankin da tun farko aka ga ɓullar cutar mai haɗari.

A cewar mahukuntan na Congo, al’ummar yankunan da ke gab da inda aka samu ɓullar cutar na rayuwa cike da fargabar makomarsu game da wannan cuta da ake ganin ɓullarta karon farko cikin shekaru 3 kuma karon farko a wannan Lardi na Kasai ciken fiye da shekaru 10.

Lardin na Kasai na da matuƙar nisa da gabashin Congo inda aka fiya ganin ɓullar cutar ta Ebola yayinda ya ke da tazarar fiye da kilomita dubu guda a birnin Kinshasa fadar gwamnati.

Baya ga Kasai an kuma gano wata mata mai juna biyu da ta harbu da cutar ta Ebola a Lardin Bulape wanda ya sanya fargabar bazuwar cutar a yankin duba da yiwuwar ta yi cuɗanya da mutane da dama.

Dr Ngashi Ngongo na cibiyar yaƙi da cutuka masu yaɗuwa ta Afrika CDC, ya ce dole a ƙarfafa yaƙi da cutar a ilahirin ƙauyukan da ke Lardunan biyu matuƙar Congo na son kakkaɓe barazanar Ebola cikin sauri.

Tuni Hukumar Lafiya ta Duniya WHO ta aike da tawaga ta musamman zuwa Congo musamman ga Lardin na Kasai don saya idanu tare da taimakawa wajen daƙile yaɗuwar cutar.

Tun daga shekarar 1976 ƙasar ta yankin tsakiyar Afrika ta fara ganin ɓullar Ebola kuma wannan ne karo na 16 da Congon ke fama da annobarta ciki har da wanda ta gani a a baya-bayan nan cikin shekarun 2018 da 2020 da ya kashe fiye da mutane dubu guda a gabashin ƙasar.

Share.
Leave A Reply

Exit mobile version