Yafiyar da shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya yi wa Maryam Sanda tare da karin mutane 174 tana sama tana dabo.

A makon da ya gabata ne, shugaban ya yiwa mutane 175 da suka haɗa da ‘yansiyasa, dilolin ƙwaya, da kuma waɗanda suka aikata kisan kai afuwa yayin taron Majalisar Ƙolin ƙasar da ya gudana.

Saidai kwatsam akaji wata sanarwa a ranar Alhamis daga ofishin ministan shari’a Lateef Fagbemi wanda shine ya jagoranci kwamitin afuwar, yana mai cewa afuwar da shugaban ƙasa yayi, sai an sake nazari akan lamarin sakamakon ƙorafe-ƙorafen mutane da suke yi.

Ofishin ministan ya ƙara da cewa duba da ƙorafe-ƙorafen jama’ar ƙasar game da mutanen da Tinubu ya yiwa afuwa, gwamnati na sake yin nazari a kai.

Haka zakila, Fagbemi ya ce babu wanda aka saki daga gidan gyaran hali, daga cikin fursunoni 175 da shugaban ƙasar ya yiwa afuwa, ko waɗanda ya yi umarnin ayi musu sassauci a hukunce-hukunce da aka yanke musu.

Share.
Leave A Reply

Exit mobile version