An dakatar da ayyukan gwamnatin tarayya a Amurka bayan kasa samun jituwa tsakanin ƴanmajalisar Democrats da Republican game da kasafin kuɗin ƙasar.

Matakin ya shafi ayyukan yau da kullum, kuma ma’aikata da dama ba za su samu albashi ba.

Wannan ne karon farko da aka rufe harakokin gwamnati bayan shekaru bakwai.

Gwamnatin za ta ci gaba da zama a rufe har sai ɓangarorin biyu sun cimma matsaya.

Ƴan Democrats na neman dawo da kuɗaɗen da aka zabtare na inshorar lafiya.

Donald Trump ya yi gargaɗin yin amfani da damar domin korar ma’aikata da kuma rage wasu ayyukan gwamnati

Share.
Leave A Reply

Exit mobile version