Jami’an agaji na ci gaba da zakulo gawawwakin mutane daga ɓaraguzan gini a Gaza yayin da janyewar dakarun Isra’ila ƙarƙashin yarjejeniyar tsagaita wuta da ta fara aiki a ranar Juma’a.

An kiyasta cewa mutum 200,000 ne suka koma gidajensu a yankin arewaci zuwa yanzu. Da dama sun ce sun kaɗu matuƙa da irin girman ɓarnar da aka yi.

Shugaban Amurka Donald Trump ya kara bayar da tabbacin cewa za a mutunta jarjejeniyar, yana mai cewa “dukkaninsu sun gaji da yaƙin, wannan lamari ya sha gaban Gaza, wannan zaman lafiya ne a Gabas ta Tsakiya.

Majalisar Ɗinkin Duniya (MDD) ta ce za ta shigar da kayan agaji cikin Gaza, kodayake ba za su wadata ba.

Yanzu mataki na gaba shi ne Hamas ta saki mutanen da ta yi garkuwa da su, Isra’ila kuma ta sako ɗaruruwan Falasdinawan da ta kama.

Share.
Leave A Reply

Exit mobile version