Mahukuntan jihar Bauchi a Najeriya sun tabbatar da mutuwar mutane 58 sanadiyyar ɓarkewar annobar cutar amai da gudawa ko kuma kwalara da ta shafi ƙananan hukumomin jihar 14 daga cikin 20.

Bayanai sun ce baya ga mutanen 58 da cutar ta kashe akwai kuma mutane aƙalla 258 da yanzu haka ke kwance sanadiyyar cutar kuma suke karɓar kulawa don ceto rayuwarsu.

Mataimakin gwamnan jihar Bauchi, Auwal Mohammed Jatau da ke bayyana haka yayin ƙaddamar da wasu kwamitin ƙwararru har guda 2 don tunƙarar wannan annoba, ya ce sake samun ɓarkewar cutar ta tayar da hankalin gwamnati matuƙa.

A cewar mataimakin gwamnan, cutar ta kwalara na sahun cutukan da za a iya daƙile yaɗuwarsu cikin gaggawa don taƙaita ɓarnarsu ga jama’a kuma wannan na daga cikin aikin kwamitocin.

Cikin jawabinsa ya ambato batutuwa masu alaƙa da tsaftar muhalli ta jiki da kuma ruwan sha a matsayin makaman da za a yi amfani da su wajen hana yaɗuwar cutar mai haɗari.

Mataimakin gwamnan na Bauchi, ya ce duk da ƙoƙarin da gwamnatin jihar ke yi wajen yaƙi da cutuka, har yanzu cutar ta amai da gudawa na sahun waɗanda suka bijire tare da zama gagarumar barazana ga jama’a.

Share.
Leave A Reply

Exit mobile version