Author: Hafsat Abubakar Adam

Hukumar Kula da Wutar Lantarki ta Najeriya (NERC) ta fara amfani da wani sabon tsari da zai bai wa masu amfani da na’urorin samar da wutar lantarki ta hasken rana (solar) damar sayar da ƙarin wutar da suke samarwa ga kamfanonin rarraba wutar lantarki. NERC ta bayyana hakan ne a wani saƙo da ta wallafa a shafinta na X, inda ta ce idan na’urar solar ta kwastoma na samar da wutar lantarki fiye da buƙatarsa, zai iya sayar da ƙarin wutar ga kamfanin rarraba lantarki (DisCo) tare da samun kuɗin da ya dace. A cewar hukumar, ana kiran wannan tsari…

Read More

Wasu ‘yan bindiga sun kai hari dakunan kwanan dalibai na Kwalejin Ilimi ta Tarayya (Federal College of Education) da ke Kaura Namoda a Jihar Zamfara, inda suka yi garkuwa da dalibai bakwai. Wani dalibin makarantar, Ibrahim Ahmad, ya bayyana cewa daya daga cikin daliban da aka sace ya samu nasarar tserewa daga hannun maharan. A cewarsa, har yanzu dalibai shida ne ke hannun ‘yan bindigar, wadanda suka hada da maza uku da mata uku. Da yake tabbatar da faruwar lamarin, kakakin rundunar ‘yan sandan Jihar Zamfara, DSP Yazid Abubakar, ya ce harin ya faru ne a daren Litinin lokacin da…

Read More