Tsohon mataimakin shugaban ƙasa kuma ɗan takarar neman kujerar shugabancin Najeriya har sau 2 a shekarun 2019 da 2023 Alhaji Atiku Abubakar ya bayyana cewa babu alamun shugaban ƙasar Bola Ahmed Tinubu zai iya magance matsalolin da suka dabaibaye jama’ar ƙasar musamman na yunwa da kuma talauci.

Ɗan adawar Atiku Abubakar wanda ya bayyana yunwar da ke addabar jama’ar Najeriya a matsayin matsalar da sam bai kamata ace ta faru ba, musamman lura da halin ƙuncin da marasa ƙarfi ke ciki.

A cewar Atiku, jama’ar Najeriya na cikin wani hali na matsi da ƙuncin rayuwa da sam bai kamata ace sun tsinci kansu a matsalar ba.

Atikun cikin wata sanarwa da kakakinsa Mr Paul Ibe ya sanyawa hannu a yau Litinin, ya ce kamata ya yi batutuwan da gwamnati zata fi mayar da hankali akai ya kasance tsaro da walwalar jama’a, maimakon haka gwamnatin ce kan gaba wajen jefa jama’arta a hali na matsi da ƙunci.

Duba da halin da Najeriya ke ciki, Atiku ya ce babu wani abin a yaba ganin yadda gwamnati ke sake jefa ƙasar cikin haɗari tare da ta’azzara yanayi na aikata manyan laifukan da suka ƙunshi damfara, ta’addanci da satar mutane don enman fansa dama shiga ƙungiyoyin asiri baya ga ta’ammali da miyagun ƙwayoyi dama tsafi da sassan jikin mutane.

Share.
Leave A Reply

Exit mobile version