Iyaye na kokawa da rashin kuɗi dai dai lokacin da makarantu ke komawa sabon zangon karatu.
Ɗimbin ɗalibai ne suka koma makarantu yau Litinin a sassan Najeriya kama daga makarantu mallakin gwamnati da kuma masu zaman kansu a sassan ƙasar ta yammacin Afrika mai fama da tarin matsalolin tattalin arziƙi da tsadar rayuwa da ta yiwa jama’arta katutu.
A wannan karon an koma makarantun a wani yanayi da farashin kayakin karatu ya sake yin tashin gwauron zabi kama daga shi kansa kuɗin makarantar da littattafan karatu dana rubutu wanda ya sanya iyaye da dama gaza wadata ƴaƴansu da abubuwan buƙata don tafiyar da harkokinsu na koyo.
Tsadar kayakin kayatun ya zo a yanayin da aljifan iyaye ya kammala ƙafewa sakamakon tsadar rayuwar da ake fama da ita.
Akwai ƙorafe-ƙorafen da ke cewa galibin makarantu masu zaman kansu sun juye zuwa kasuwanci maimakon bayar da ilimin tare da barin iyaye a halin ƙaƙanikayi.
Can a makarantun gwamnati kuwa duk da taɓarɓarewar tsarin na bayar da ilimi da ma rashin kyawun azuzuwa ko muhallin koyar da yaran koma rashin malamai, duk da haka shugabannin makarantun kan nemi kuɗaɗe daga hannun iyaye.
Tsarin koyarwa ko bayar da ilimi musamman a makarantun masu ƙaramin ƙarfi na fama da gagarumar matsala yayinda halin da ake ciki na matsain rayuwa kuma ke yiwa karatun yara shaƙar mutuwa.
