Kwamitin tsaro na Majalisar ɗinkin duniya zai yi zama kan harin Isra’ila a Qatar
Kowanne lokaci a yau Alhamis kwamitin tsaro na Majalisar ɗinkin duniya ke shirin yin wani zama na musamman don tattaunawa kan harin da Isra’ila ta kai Qatar da nufin kisan jagororin ƙungiyar Hamas.
Yayin wannan zama na kwamitin tsaron majalisar wanda Korea ta kudu ke jagoranta a yanzu, mambobin majalisar za su tafka muhawara kan harin na Isra’ila kan Qatar wanda Doha ta bayyana da keta dokokin ƙasa da ƙasa.
Harin na ranar Talata ya faru ne lokacin da ake tsaka da tattaunawa kan ƙoƙarin cimma yarjejeniyar tsagaita wuta a yaƙin da Isra’ilar ta shafe fiye da shekaru 2 tana yi kan Falasɗinawa da zuwa yanzu ta kashe mutanen da yawansu ya haura dubu 60.
A jiya Laraba aka tsara gudanar da zaman na gaggawa, amma wata sanarwar Majalisar ta sanar da ɗage shi zuwa yau Alhamis.
Tuni Qatar ta sanar da janyewa daga ci gaba da shiga tsakani don kawo ƙarshen wannan yaƙi a wani yanayi da Doha ke ci gaba da musanta iƙirarin Amurka na cewa ta bata sanarwa game da harin na Isra’ila tun gabanin faruwarsa.
