Masana a ɓangaren kiwon lafiya sun koka da yawaitar mace-macen fuju’a ko kuma mutuwar kwaf-ɗaya da ake ganin ta’azzararta a sassan Najeriya, ta yadda mutane kan yanke jiki su mutu nan ta ke ba tare da alamu ko jinyar wata cuta ba.
Masanan sun bayyana yawaita mutuwar ta kwaf ɗaya a matsayin babban ƙalubalen lafiya da ke buƙatar ɗaukar matakan gaggawa musamman ta fannin ganin mutane sun rungumi tsarin duba lafiyarsu akai-akai.
Duk da cewa babu cikakkun alƙaluman mutanen da ke mutuwar ta kwaf-ɗaya a sassan Najeriya, amma a baya-bayan nan ana ganin yawaitar masu wannan mutuwa ta Fuju’a a matakai daban-daban kama daga fitattu da kuma ɗaiɗaikun jama’a.
Wasu bayanai da jaridar Daily Trust ta tattara sun nuna ƙaruwar wannan matsala cikin watanni 9 da suka gabata, inda bayanai ke nuna yadda ɗimbin ƴan Najeriya kama daga Matasa da Tsaffi da masu riƙe da madafun iko ke yanke jiki suna faɗuwa tare da mutuwa nan take ba tare da wata cuta ba.
Bayanan sun nuna cewa waɗanda wannan mutuwar ta kwaf-ɗaya ko kuma fuju’a ta shafa sun ƙunshi ɗalibai, ƴan ƙasuwa da malaman jami’a dama ƴan wasan motsa jiki baya da manoma dama ƙusoshin gwamnati kama daga waɗanda suka yi ritaya da waɗanda ke bakin aiki.
Bayanan sun ci gaba da nuna cewa wasu daga cikin waɗanda suka yi mutuwar ta kwaf-ɗaya sun mutu nan take bayan faɗuwa yayinda wasunsu suka mutu bayan kai su ga asibitoci.
Masanan da ke alaƙanta mutuwar ta kwaf-ɗaya da cutukan da ke da alaƙa da kodai zuciya ko kuma lumfashi, koma wasu kwantattun cutuka da jama’a ke da su ba tare da ɗaukar matakai na kulawar lafiya, sun ce ya zama wajibi al’umma su rungumi tsarin duba lafiya ko da basu jin kowanne ciwo.
