Wata alƙaliyar kotun Amurka ta soki matakin Donald Trump na tisa ƙeyar ƴanciranin ƙasashen yammacin Afrika da suka ƙunshi ƴan Najeriya da Gambia zuwa Ghana.
Alƙaliyar kotun gundumar Washington Tanya Chutkan ta ce akwai hujjoji daga lauyoyin ƴanciranin da ke nuna cewa zasu fuskanci azabtarwa da ko kuma miƙasu gaban kotu matuƙar aka mayar da su ƙasashensu.
Hasalima Alƙaliyar ta bayyana tsarin miƙa ƴanciranin ga wata ƙasa a matsayin abin da ya saɓawa doka ya kuma saɓawa yardar da duniya ke da shi ga Amurka wajen samun kariya daga dukkanin barazana.
Mai shari’a Chutkan ta buƙaci gwamnatin Amurka ta yi gagagwar umartar Ghana kan ta kaucewa miƙa ƴanciranin ga ƙasashensu na asali saboda kaucewa azabtarwar da za su iya fuskanta.
A cewar alƙaliyar da cikakken sani ne gwamnatin Trump ta kaucewa bin tanadin dokar ƴancirani ƙarƙashin kundin tsarin mulkin Amurka, tare da yin gaban kanta wajen tisa ƙeyar baƙin hauren.
