Shugaban Amurka Donald Trump ya bukaci ƙasashen da ke cikin ƙungiyar Tsaro na NATO da su dakatar da cinikin mai da Rasha, sannan sun sanya takunkumi ga ƙasar, kafin Amurka itama ta bi sahu da irin na ta takunkuman.

Shugaban na Amurka Donald Trump ya ce ƙasar a shirye ta ke  ta sanya gagarumin takunkumi ga Rasha kan yakinta da Ukraine muddun ƙasashen da ke cikin ƙungiyar NATO su ka fara da sanya irin nasu takunkumin da kuma dakatar da sayen mai na ƙasar.

Har ila yau, shugaba Trump ya kuma bukaci mambobin ƙungiyar ƙasashen da ke yankin tekun Atlantika, su yi la’akari da dora harajin kashi 50 zuwa kashi 100 ga ƙasar China, a matsayin hanyar da za ta taimaka wajen kawo ƙarshen yakin Rasha a Ukraine.

A shirye nake da in sanya manyan Takunkumi kan Rasha, muddun dukkan ƙasashen NATO suka amince, kuma suka fara, ɗaukar irin wannan mataki, da kuma lokacin da dukkan ƙasashen NATO suka daina sayen man fetur daga Rasha

Trump wallafa hakan a shafinsa na dandalin sada zumunta na Truth, wanda ya bayyana a matsayin wasika ga dukkanin mambobin ƙungiyar NATO da ma duniya baƙi ɗaya.

Trump ya sha yi wa Rasha barazanar ƙarin takunkumi – ciki har da wanda ya yi mata a ƙarshen makon da ya gabata bayan da Kremlin ta ƙaddamar da hare-hare ta sama mafi girma a kan Ukraine, amma har yanzu bai ɗauki wani mataki ba, lamarin ke fusata Kyiv.

Shugaban wanda ya gana da takwaransa na Rasha Vladimir Putin a watan da ya gabata a wani taro a Alaska, ya bayyana sayan man fetur da ƙasashen NATO ke yi na Rasha a matsayin abin mamaki, ya kuma ce hakan yana raunana karfin gogayyar kasuwancinsu da Moscow.

Mista Trump ya ce,

“muddun kawancen ƙasashen mai membobi 32 suka ɗauki shawararsa, to lallai wannan yaƙi zai ƙare cikin ƙanƙanin lokaci, amma kuma idan ba haka ba, to suna ɓata lokaci na ne kawai”.

Share.
Leave A Reply

Exit mobile version