Aƙalla mutane dubu 62 da 700 aka tabbatar da cewa sun mutu sakamakon cutuka masu alaƙa da tsananin zafi a ƙasashen nahiyar Turai cikin shekarar da ta gabata ta 2024 kamar yadda mujallar lafiya ta Nature Medicine ta wallafa a farkon makon nan.
Masu bincike a cibiyar Global Health da ke Barcelona a Spain waɗanda ke bibiyar mace-macen da ake fuskanta sanadiyyar zafin sun ce daga shekarar 2022 zuwa 2024 mutane dubu 181 daga ƙasashe 32 tsananin zafin ya kashe a Turai.
Rahoton ya bayyana cewa Mata da Tsofaffi da kuma ƙananan yara su ne kan gaba da yanayin na tsananin zafi ke kashewa a ƙasashen nahiyar ta Turai.
A cewar rahoton daga ranar 1 ga watan Yunin zuwa 30 ga watan Satumban 2024, mace-macen da ake fuskanta sanadiyyar zafin ya ƙaru da kashi 23 daga yadda aka saba gani a shekarun da suka gabata.
Rahoton ya bayyana cewa shekarar ta 2024, ta kashe tarin mutane saboda tsanantar zafin kodayake har yanzu wannan adadi bai kai wanda aka gani a shekarar 2022, inda aka ga mutuwar mutane dubu 67 da 900 da zafin ya kashe.
