Amnesty ta bayyana wasu kamfanoni 15 da ke ɗaukar nauyin yaƙin Isra’ila a Gaza

Ƙungiyar kare haƙƙin ɗan adam ta Amnesty International ta fitar da wani rahoto da ke nuna wasu manyan kamfanonin duniya 15 a matsayin waɗanda ke goyon bayan kisan ƙare dangin da Isra’ila ke yi a Gaza.

Amnesty International ta ce kamfanonin 15 na taimakawa Isra’ila wajen take haƙƙoƙin ɗan adam tare da keta dokokin ƙasa da ƙasa a kisan ƙare dangin da ƙasar ke ci gaba da aikatawa a Gaza yayin yaƙin kusan shekaru 2 da ta ke da mayaƙan Hamas.

Rahoton na Amnesty ya ce waɗannan kamfanoni na taimakawa Isra’ilan ta hanyoyi daban-daban, kama da cinikayyar makamai ko kasuwanci ko kuma zuba jari, inda babbar sakatariyar ƙungiyar Agnès Callamard, ke cewa a tsawon lokacin da Isra’ila ta ɗauka tana aikata kashe-kashe a Gaza, ya ɗore ne kaɗai da taimakon manyan kamfanonin daga sassa daban-daban na duniya waɗanda ke tallafawa ɗorewar tattalin arziƙinta da kuma kasuwancinta dama sauran kayakin yaƙi.

A cewar Amnesty na gaba-gaba a cikin waɗannan kamfanoni shi ne Boeing na Amurka wanda ke wadata ƙasar da jiragen yaƙi, sai kuma kamfanonin fasaha na Lockheed Martin da Palantir Technologies kana fitaccen kamfanin nan mallakin Isra’ila na Elbit Systems kana Rafael Advanced Defense Systems da kuma masana’antar jiragen yaƙi da ke samar da jirage marasa matuƙi ta Israel Aerospace Industries kana Corsight da Mekorot sannan kamfanin China Hikvision da kuma HD Hyundai na Korea ta kudu kana kamfanin gine-gine na Spain wato Construcciones y Auxiliar de Ferrocarriles da ake kira (CAF).

Amnesty ta ce kamfanonin sun ci gaba da shigarwa Isra’ila da tarin makamai duk kuwa da masaniya kan ta’adin da ƙasar ke yi wajen take haƙƙin ɗan adam.

Share.
Leave A Reply

Exit mobile version