Tsohon gwamnan Kano ya yabawa gwamnan Kano Abba Kabir Yusuf bisa ƙoƙarin sa akan harkokin ilimi a jihar.

Hakan ya biyo bayan da aka saki saka makon jarabawar kammala karatun sakandare ‘NECO’ inda aka bayyana ɗaliban jihar Kano ne ke kan gaba wajan samun nasar.

Tsohon Gwamnan Jihar Kano, Engr. Rabi’u Musa Kwankwaso ya taya daliban Kano murna bisa samun nasara a jarrabawar kammala sakandare ta kasa (SSCE) da Hukumar NECO ta gudanar a shekarar 2025.

Kwankwaso ya ce wannan nasara ba ta zo a banza ba illa sakamakon jajircewar Gwamnatin Jihar Kano karkashin jagorancin Mai Girma Gwamna Alhaji Abba Kabir Yusuf wajen zuba jari a fannin ilimi cikin shekaru biyu da suka gabata.

Ya bayyana cewa, “Lokutan da NECO ke rike sakamakon daliban Kano saboda rashin biyan kudade sun wuce, kuma yanzu ga amfanin kokarin gwamnati yana bayyana.”

Kwankwaso ya kuma bukaci gwamnati da sauran masu ruwa da tsaki a harkar ilimi su ci gaba da dagewa wajen kula da wannan matsayi, tare da kara himma domin inganta ilimi a nan gaba.

Share.
Leave A Reply

Exit mobile version