Shugaban sashen ilimin Ƙasa (Geography) na Jami’ar Northwest da ke Jihar Kano, Dakta Nazifi Umar Alaramma ya yi kira ga gwamnatin taraiya da ta sanya darasin ‘ Geography’ ya zama wajibi ga daliban sakandare a cikin manhajar karatu ta ƙasa saboda muhimmacinsa.

DAILY NIGERIAN HAUSA ta tuna cewa a shekarar 2013 ne gwannatin tarayya ta cire darasin ilimin Geography a matsayin dole ga ɗaliban sakandare Inda ya koma a matsayin zabi.

Saidai kuma Alaramma, a taron manema labarai gabanin Babban Taron Kungiyar Masana Ilimin Ƙasa ta Najeriya (Association of Nigerian Geographers, ANG) da jami’ar Northwest za ta karbi bakuncinsa na 2025, ya baiyana cewa za’a tattauna batun neman dawo da wajabta ilimin Geography a matsayin wajibi ga dalibai.

Ya ce taron karo na 65 zai karbi manyan baki da masana ilimin ƙasa daga jihohin Najeriya da dama domin baje basirarsu.

Dakta Alaramma ya kuma baiyana cewa za a tattauna mahimman batutuwa da suka shafi cigaban kasashen duniya musamman masu tasowa.

Taken taron na ANG na bana shi ne :

“Binciken raunin yanayi,da bambancin tattalin arziki da rashin daidaito a cikin al’umma a kasashe masu tasowa.”

A yayin taron na manema labaran, Dakta Alaramma wanda shine mai shirya wajen taron ya ce kamar yadda aka dawo da wajabtawa daliban sakandire koyon darasin ilimin Tarihi wato History a Najeriya, ya kamata gwannatin tarayya ta dauki irin wannan matakin akan Geography.

Dr. Nazifi Umar Alaramma, ya yi kira ga gwamnati da masu tsara manufofin ilimi da su dawo da darasin Geography a matsayin darasi dole ga ɗalibai.

Yace akwai fatan cewa masana da masu ruwa da tsaki zasu gabatar da wannan bukata a yayin taron da za’a gudanar a Jami’ar Northwest a Kano.

A cewarsa, Geography darasi ne da yake da muhimmanci wajen fahimtar yadda duniya ke tafiya, da dangantakar mutum da muhalli, da kuma matsalolin da ke shafar rayuwar yau da kullum, irin su dumamar yanayi, rarrabuwar albarkatu da ƙauracewar jama’a daga wuri zuwa wuri.

Share.
Leave A Reply

Exit mobile version