Matasa shida daga Najeriya ne suka samu nasarar lashe gasar Hadisi da Gidauniyar Sarkin Moroko Mohammed na shida ta shiryawa Malaman Afrika.
Ɗaya daga cikin alkalan gasar, Dr. AbdulGaniyu Tijani, ne ya bayyana hakan yayin bikin rufe gasar da aka gudanar a birnin Abuja a ranar Asabar.
Ya ce waɗanda suka lashe kyautar a rukuni na farko su ne Fatima Turbo, Muhammad Ibrahim, da Abubakar Abba, dukkansu daga jihar Borno.
A rukuni na biyu kuwa, akwai Saleh Al-Amin daga Borno, Ahmed Kolawole daga Kwara, da Khalifah Jibril daga Kaduna sune suka fito zakaru.
Kowane rukuni mutane uku ne suka yi nasara, inda na farko suka samu kyautar Naira dubu 250,000, na biyu suka samu Naira 200,000, sannan na uku suka samu 150,000.
